1. Sai mazaunan Urushalima suka naɗa Ahaziya, autansa, ya gāji gadon sarauta, saboda ƙungiyar mutanen da suka zo tare da Larabawa a sansanin sun karkashe dukan 'yan'uwansa maza. Ahaziya ɗan Yoram Sarkin Yahuza, ya fara mulki.
2. Ahaziya yana da shekara arba'in da biyu sa'ad da ya ci sarauta, ya kuwa yi mulki shekara guda a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Ataliya jikar Omri.