17. Sarkin Isra'ila fa ya ce wa Yehoshafat, “Ban faɗa maka ba, cewa ba zai yi annabcin alheri game da ni ba, sai na rashin alheri?”
18. Sai Mikaiya ya ce, “Ji maganar Ubangiji, na ga Ubangiji yana zaune a bisa kursiyinsa, dukan rundunan sama suna tsaye dama da shi da hagu da shi.
19. Sai Ubangiji ya ce, ‘Wa zai ruɗi Ahab, Sarkin Isra'ila, don ya haura zuwa Ramot-gileyad ya fāɗi?’ Sai wannan ya faɗi abu kaza, wancan kuma ya faɗi abu kaza.
20. Sai wani ruhu ya zo ya tsaya a gaban Ubangiji, ya ce, ‘Ni zan ruɗe shi.’ Sai Ubangiji ya ce masa, ‘Ta ƙaƙa?’