2 Tar 16:3-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. “Bari mu haɗa kai, da ni da kai kamar yadda ubana da naka suka yi. Ga shi, na aika maka da azurfa da zinariya. Ka tafi ka warware haɗa kan da yake tsakaninka da Ba'asha, Sarkin Isra'ila, don ya janye ya rabu da ni.”

4. Ben-hadad kuwa ya kasa kunne ga sarki Asa, ya aika da shugabannin rundunan sojojinsa suka yi yaƙi da biranen Isra'ila. Suka ci Iyon, da Dan, da Abel-bet-ma'aka, da dukan biranen ajiya na Naftali.

5. Da Ba'asha ya ji haka, sai ya daina gina Rama, ya bar aikin da yake yi.

2 Tar 16