3. Ubangiji kuwa ya husata da jama'ar Isra'ila, sai ya dinga ba da su a hannun Hazayel Sarkin Suriya, da hannun Ben-hadad ɗan Hazayel.
4. Sai Yehowahaz ya roƙi Ubangiji, Ubangiji kuwa ya ji shi, gama ya ga wahalar da Isra'ilawa suke ciki, wato yadda Sarkin Suriya yake musguna musu.
5. Saboda haka Ubangiji ya ba jama'ar Isra'ila maceci, suka kuwa kuɓuta daga ƙangin Suriyawa, suka zauna a gidajensu lafiya kamar dā.