19. Sauran ayyukan Yowash da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.
20. Fādawansa suka ƙulla maƙarƙashiya, suka kashe shi a gidan da yake Millo, a kan hanyar da ta nufi Silla.
21. Yozakar ɗan Shimeyat, da Yehozabad ɗan Shemer su ne fādawansa da suka kashe shi. Aka binne shi a makabartar kakanninsa cikin birnin Dawuda. Amaziya ɗansa ya gāji sarautarsa.