26. “Kai, ya Ubangiji, amintacce ne ga waɗanda suke da aminci,Nagari ne kuma ga waɗanda suke cikakku.
27. Mai Tsarki ne kai ga waɗanda suke tsarkaka,Amma kana gāba da waɗanda suke mugaye.
28. Kakan ceci masu tawali'u,Amma kakan ƙasƙantar da masu girmankai.
29. “Ya Ubangiji, kai ne haskena,Kana haskaka duhuna.
30. Ka ba ni ƙarfi don in auka wa abokan gābana,Da iko domin in murƙushe tsaronsu.
31. “Allahn nan cikakke ne ƙwarai,Maganarsa tabbatacciya ce!Kamar garkuwa yakeGa dukan masu neman kiyayewarsa.
32. Ubangiji shi kaɗai ne Allah,Allah ne kaɗai madogararmu.