2 Kor 3:13-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Ba kamar Musa muke ba, wanda ya rufe fuskarsa da mayafi, don kada Isr'ailawa su ga ƙarewar ɗaukakar nan mai shuɗewa.

14. Amma hankalinsu ya dushe, domin har ya zuwa yau, in ana karatun Tsohon Alkawari, mayafin nan har yanzu ba a yaye yake ba, domin ba ya yayuwa sai ta wurin Almasihu kaɗai.

15. Hakika har ya zuwa yau, duk lokacin da ake karatun littattafan Musa, sai mayafin nan yakan rufe zukatansu.

2 Kor 3