1 Tim 5:22-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Kada ka yi garajen ɗora wa kowa hannu, kada kuwa zunuban waɗansu su shafe ka. Ka tsare kanka a tsarkake.

23. A nan gaba ba ruwa kaɗai za ka sha ba, sai dai ka sha ruwan inabi kaɗan saboda cikinka, da kuma yawan laulayinka.

24. Zunuban waɗansu mutane a fili suke, tun ba a kai gaban shari'a ba. Zunuban waɗansu kuwa, sai daga baya suke bayyana.

25. Haka kuma, kyawawan ayyukan waɗansu a fili suke, waɗanda ba haka suke ba, ba za su tabbata a ɓoye ba.

1 Tim 5