1 Tas 4:12-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. domin ku zama masu mutunci ga waɗanda ba masu bi ba, kada kuma ku rataya a jikin kowa.

13. Amma 'yan'uwa, ba mu so ku jahilta game da waɗanda suka yi barci, don kada ku yi baƙin ciki kamar yadda sauran suke yi, marasa bege.

14. Tun da muka gaskata Yesu ya mutu, ya kuwa tashi, haka kuma albarkacin Yesu, Allah zai kawo waɗanda suka yi barci su zo tare da shi.

15. Muna kuwa shaida muku bisa ga faɗar Ubangiji, cewa mu da muka wanzu, muke kuma a raye har ya zuwa komowar Ubangiji ko kaɗan ba za mu riga waɗanda suka yi barci tashi ba,

1 Tas 4