77. Daga na kabilar Zabaluna, an ba sauran Lawiyawa, wato 'ya'yan Merari, maza, Rimmon duk da makiyayarta, da Tabor duk da makiyayarta.
78. Daga na kabilar Ra'ubainu a hayin Urdun a Yariko, wato gabashin Urdun, an ba da Bezer ta cikin jeji duk da makiyayarta, da Yahaza duk da makiyayarta,
79. da Kedemot duk da makiyayarta, da Mefayat duk da makiyayarta.