1 Tar 5:21-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Sai suka kwashe dabbobinsu, raƙuma dubu hamsin (50,000), da tumaki dubu ɗari biyu da dubu hamsin (250,000), da jakuna dubu biyu (2,000), da kuma mutane dubu ɗari (100,000).

22. Aka karkashe mutane da yawa, domin yaƙin na Allah ne. Sai suka gāje wurin zamansu, har lokacin da aka kai su bauta.

23. Mutanen rabin kabilar Manassa suna da yawa, sun zauna a ƙasar, daga Bashan har zuwa Ba'al-harmon, da Senir, da Dutsen Harmon.

24. Waɗannan su ne shugabannin gidajen kakanninsu, Efer, da Ishi, da Eliyel, da Azriyel, da Irmiya, da Hodawiya, da Yadiyel. Su jarumawa ne na gaske, masu suna, su ne shugabannin gidajen kakanninsu.

1 Tar 5