1 Tar 29:11-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Girma, da iko, da daraja, da nasara, da ɗaukaka duk naka ne, ya Ubangiji, gama dukan abin da yake cikin sammai da duniya naka ne. Mulki kuma naka ne, ya Ubangiji. Kai ne Maɗaukaki duka.

12. Dukan wadata da girma daga gare ka suke, kai kake mulki da dukan iko da ƙarfi. Kai ne kake da iko ka ba mutum iko da ƙarfi.

13. Yanzu ya Allahnmu, muna gode maka muna kuma yabon sunanka mai daraja.

1 Tar 29