1 Tar 26:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ƙungiyoyin masu tsaron ƙofofi ke nan. Na wajen Kora shi ne Shallum ɗan Kore, daga cikin iyalin Ebiyasaf.

2. Shallum kuwa yana da 'ya'ya maza, su ne Zakariya, da Yediyayel, da Zabadiya, da Yatniyel,

3. da Elam, da Yehohanan, da Eliyehoyenai, su bakwai ke nan.

1 Tar 26