22. Segub shi ne mahaifin Yayir wanda yake da birane ashirin da uku a ƙasar Gileyad.
23. Amma sai Geshur da Aram suka ƙwace garuruwan Hawwotyayir ɗin daga gare su, har da Kenat da ƙauyukanta, garuruwa sittin. Duk waɗannan su ne zuriyar Makir mahaifin Gileyad.
24. Bayan rasuwar Hesruna, Abaija, matarsa, ta haifa masa Ashur, mahaifin Tekowa.
25. 'Ya'yan Yerameyel ɗan farin Hesruna, su ne Arama ɗan fari, sa'an nan Buna, da Oren, da Ozem, da Ahaija.
26. Sai Yerameyel ya auro wata mace, sunanta Atara. Ita ce mahaifiyar Onam.
27. 'Ya'yan Arama, ɗan farin Yerameyel, su ne Ma'az, da Yamin, da Eker.
28. 'Ya'yan Onam, maza, su ne Shammai da Yada. 'Ya'yan Shammai, maza, su ne Nadab da Abishur.
29. Sunan matar Abishur Abihail, ta haifa masa Aban da Molid.