16. 'Yan'uwansu mata kuwa su ne Zeruya da Abigail.'Ya'yan Zeruya, maza, su ne Abishai, da Yowab, da Asahel, su uku ke nan.
17. Abigail ta haifi Amasa. Mahaifin Amasa shi ne Yeter daga zuriyar Isma'ilu.
18. Azuba, matar Kalibu ɗan Hesruna ta haifa masa 'ya'ya maza. Matarsa Yeriyot kuma ta haifi 'ya'ya maza, su ne Yesher, da Shobab, da Ardon.
19. Sa'ad da Azuba ta rasu sai Kalibu ya auri Efrata wadda ta haifa masa Hur.
20. Hur shi ne mahaifin Uri, Uri kuwa shi ne mahaifin Bezalel.
21. Bayan haka sai Hesruna ya shiga wurin 'yar Makir mahaifin Gileyad, wadda ya aura sa'ad da yake da shekara sittin da haihuwa. Ta haifa masa Segub.