1 Tar 19:12-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Yowab ya ce wa Abishai, “Idan Suriyawa sun fi ƙarfina, to, sai ka taimake ni, amma idan Ammonawa sun fi ƙarfinka, to, sai in taimake ka.

13. Mu yi ƙarfin hali, mu yi jaruntaka saboda jama'armu da biranen Allahnmu. Bari Ubangiji ya yi abin da ya ga ya yi masa kyau.”

14. Yowab da jama'ar da suke tare da shi suka matso don su yi yaƙi da Suriyawa, sai Suriyawa suka gudu daga gabansu.

15. Da Ammonawa suka ga Suriyawa sun gudu, su ma suka gudu daga gaban Abishai, ɗan'uwan Yowab, suka shiga birni. Sa'an nan Yowab ya komo Urushalima.

16. Da Suriyawa suka ga Isra'ilawa sun ci su da yaƙi sai suka aiki manzanni suka kira Suriyawa waɗanda suke hayin kogi. Shobak shugaban sojojin Hadadezer ne yake shugabantarsu.

1 Tar 19