10. Sai Dawuda ya roƙi Allah, ya ce, “In tafi in yi yaƙi da Filistiyawa? Za ka bashe su a hannuna?”Ubangiji kuwa ya amsa masa, ya ce, “Ka haura, gama zan bashe su a hannunka.”
11. Sai suka haura zuwa Ba'al-ferazim, Dawuda kuwa ya ci su da yaƙi a wurin. Sai ya ce, “Allah ya raraki maƙiyana ta hannuna, kamar yadda ruwa yakan rarake ƙasa.” Don haka aka sa wa wurin suna Ba'al-ferazim.
12. Filistiyawa suka gudu suka bar gumakansu a wurin. Dawuda kuwa ya yi umarni, aka ƙone su duka.
13. Filistiyawa kuma suka sāke kawo yaƙi a kwarin.
14. Dawuda ya sāke yin roƙo ga Allah, Allah kuwa ya ce masa, “Kada ka hau zuwa wurinsu, ka kewaye ka ɓullo musu ta baya daura da itatuwan tsamiya.