1 Tar 13:9-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Sa'ad da suka kai masussukar Kidon, sai Uzza ya miƙa hannunsa don ya riƙe akwatin alkawarin saboda gargada.

10. Sai Ubangiji ya husata da Uzza, ya buge shi, ya mutu nan take a gaban Allah, saboda ya miƙa hannunsa ya kama akwatin alkawari.

11. Sai Dawuda ya ɓata ransa saboda da Ubangiji ya hukunta Uzza da fushi, sai ya sa wa wannan wuri suna Feresa-uzza, wato hukuncin Uzza.

12. Sa'an nan Dawuda ya ji tsoron Allah, ya ce, “Ƙaƙa zan kawo akwatin alkawarin Allah a gidana?”

1 Tar 13