1 Tar 13:8-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Sai Dawuda da dukan Isra'ilawa suka yi rawa da iyakar ƙarfinsu a gaban Allah, suna raira waƙoƙi suna kaɗa, garayu, da molaye, da ganguna, da kuge, suna busa ƙaho.

9. Sa'ad da suka kai masussukar Kidon, sai Uzza ya miƙa hannunsa don ya riƙe akwatin alkawarin saboda gargada.

10. Sai Ubangiji ya husata da Uzza, ya buge shi, ya mutu nan take a gaban Allah, saboda ya miƙa hannunsa ya kama akwatin alkawari.

1 Tar 13