1 Sar 3:1-2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sulemanu ya gama kai da Fir'auna, Sarkin Masar, ta wurin aure, domin ya auri 'yar Fir'auna, ya kawo ta birnin Dawuda kafin ya gama ginin gidan kansa, da Haikalin Ubangiji, da garun Urushalima.

2. Mutane suka yi ta miƙa hadayu a al'amudai dabam dabam, domin ba a gina haikalin Ubangiji ba tukuna.

1 Sar 3