2. Sai ya aika da jakadu zuwa cikin birni wurin sarki Ahab na Isra'ila, ya ce masa, “In ji Ben-hadad,
3. ‘Azurfarka da zinariyarka nawa ne, matanka kuma mafi kyau da 'ya'yanka nawa ne!’ ”
4. Ahab Sarkin Isra'ila kuwa ya amsa, ya ce, “Ya maigirma sarki, kamar yadda ka faɗa, ni naka ne da dukan abin da nake da shi.”
5. Jakadun kuwa suka sāke komawa suka ce wa Ahab, “Ben-hadad ya ce, ‘Na aika maka ka ba ni azurfarka, da zinariyarka, da matanka, da 'ya'yanka.
6. Banda haka kuma zan aiko barorina wurinka gobe war haka su bincike gidanka da gidajen fādawanka, su kwashe dukan abubuwan da kake ganin darajarsu su tafi da su.’ ”