1. A lokacin nan Abaija ɗan Yerobowam ya kwanta ciwo.
2. Yerobowam kuwa ya ce wa matarsa, “Ki tashi, ki ɓad da kama don kada a sani ke matata ce, sa'an nan ki tafi Shilo wurin Ahija, annabin nan wanda ya ce mini zan sarauci jama'an nan.
3. Ki ɗauki malmalar abinci guda goma, da waina, da kurtun zuma, ki tafi wurinsa. Zai faɗa miki abin da zai faru da yaron.”
4. Matar kuwa ta yi haka. Ta tashi ta tafi Shilo a gidan Ahija. Ahija ba ya gani, saboda tsufa.