27. In wani a cikin marasa ba da gaskiya ya kira ku cin abinci, kuka kuwa yarda ku tafi, sai ku ci duk irin da aka sa a gabanku, ba tare da tambaya ba saboda lamiri.
28. In kuwa wani ya ce muku, “An yanka wannan saboda gunki ne fa,” to, kada ku ci, saboda duban mutuncin wannan mai gaya muku, da kuma saboda lamiri,
29. nasa lamiri fa na ce, ba naka ba. Don me fa lamirin wani zai soki 'yancina?
30. In na yi godiya ga Allah a kan abincina, saboda me za a zarge ni a kan abin da na ci da godiya ga Allah?